RIKICIN TARABA: Mutane 10 sun rasa rayukansu

1

Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a rikicin jihar Taraba da ya barke yau Talata.

Kamar yadda rahotanni ya zo, ‘Yan Kabilan Mummuye ne suka afka ma wadansu kauyukan Fulani da ya hada da garuruwan Lushi, Sakuwa ,Hore Ladde da Garin Dogo.

Gidaje da dama ne aka kona a rikicin Talata din.

Kamar yadda Hukumar ‘yan sandan Jihar Taraba ta sanar, wadansu matasa ne ‘yan asalin Kabilar Mummuye suka farma kauyukan Bonja, da Mayo-Kunga wanda garuruwan Fulani ne. Da ga nan ne kuma suma suka ne mi daukan fansa akan hakan in da har mutane goman suka rasa rayukansu a rikicin.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya umurci mutanen yankin musamman mabiya addinin kirista da su ta shi tsaye domin kare kansu akan hare-haren da basu ji ba basu gani ba.

Ya fadi hakanne a lokacin da yake jawabi akan rikin Kudancin Kaduna a Jalingo.

Hujumar ‘Yansanda ta tabbatar da hasaran gidaje sama da 75.

Share.

game da Author