Sojojin Najeriya 800 ne za’a aika kasar Gambiya domin tilasta ma shugaban kasar Yahaya Jammeh ya sauka daga kan karagar Mulkin kasar bayan amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da ya yi bayan zabe.
Majiyar mu ta sanar da wannan gidan jarida PREMIUM TIMES cewa sojoji 800 ne aka zabo inda za a kaisu jihar Kaduna domin samun horo na musamman akan hakan.
Yahya Jammeh ya ce ba zai sauka daga kan karagar mulki ba saboda zargin da yayi cewa an yi murdiyya a zaben.
Kungiyar ECOWAS ta na shirin zuwa kasar Gambiya din akan jagorancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gobe Juma’a domin cigaba da tattaunawa da gwamnatin wajen ganin Jammeh ya hakura ya sauka kamar yadda dokar kasar ta gindaya.