Hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da harin da aka kai garuruwan wasu Fulani mazauna kauyukan Zankan da ke karamar hukumar Kaura,kudancin jihar Kaduna.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Aliyu Usman ya kuma sanar da cewa an kashe mutum daya a harin sannan anji wa mutane 5 raunuka.
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan suna nan suna bin diddigi akan abinda ya faru da kuma zakulo duk wadanda suka aikata wannan aiki domin a hukunta su.
Yace an kai harin ranar asabar da karfe 8:30 na dare.