Mutanen Najeriya sun koka da rashin Kananzir

0

Rahoton ma’aikatar Kididdiga wato ‘NBS’ ya nuna yadda ‘yan Najeriya musamman mazaunan jihohin Abia, Osun da Ondo su ka koka da tsadan kudin kananzir a kasar musamman a shekarar 2016.

Rahotan ya nuna cewa a shekarar 2016 mutane a jihar Abia sun sayi litan kananzir akan Naira 211, jihar Osun da Ondo kuwa sun sayi litan kananzir akan Naira 210. Duk tsadar da yayi wasu jihohin a yankin arewacin Najeriya sun siya kanazir din da sauki. Jihohi kamar su Gombe da Kogi sun sayi litan kananzir akan Naira 185 sai kuma jihar Sokoto da birnin tarayya sun sayi litan kananzir akan Naira 180 a shekarar bara.

Bayan haka a makon da ya wuce kasar ta yi fama da karancin kananzir inda yayi tashin gwuron zabi. A dalilin haka ya sa mutane suka koma amfani da itace da Iskar Gas.

A yanzu haka jihohin da suka fi fama da matsalar karancin kananzir sun hada da jihohin Kaduna,Cross River da kuma wasu yankunan garin Zariya, Legas da na Ondo.

Share.

game da Author