Akalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu, inda wasu 8 suka jikkita a wata hari da wasu yan bindiga suka kai wani masallaci da ke Quebec kasar Canada.
Kamar yadda gidan Talabijin din CNN ta rahoto, mutane biyu cikin bakaken kaya ne suka kai wa masallacin hari.
Jami’an tsaro sun tabbatar da kama mutane biyu da ake zargin su ne suka kai hari.
Kwamitin masallacin sun yi gargadin yada jita-jita akan abun da ya faru cewa jami’an tsaro kasan sun fara bincike akai.