Mutane 50 ne suka rasa rayukansu a harin Sojin saman Najeriya bisa Kuskure

1

An tabbatar da rasuwan mutane 52 da wadansu 120 da suka samu raunuka daba dabam a harin sojin saman Najeriya a sansanin ‘yan gudun hijra da ke garin Ran, jihar Borno kamar yadda Kungiyar likitocin sa kai ta MSF ta sanar.

Wannan hari an kaishi ne bisa kuskure.

Kwamanda a rundunar sojin Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce matukin jirgin yakin ya kai hari kan mutanen ne bisa kuskure bayan ya dauka cewa taron yan Boko Haram ne.

Kungiyar likitocin sa kai ta MSF ta ce mutane 52 ne suka rasa rayukansu, yayin da mutane 120 suka samu raunuka dabam dabam wanda ya hada da wadansu daga cikin ma’aikatan bada agaji da suke aiki a sansanin.

Ita ma kungiyar bada agaji ta Red Cross ta tabbatar da mutuwar ma’aikatanta guda 6.

Share.

game da Author