Hukumar bada agaji na gaggawa, NEMA ta sar da cewa mutane 204 suka rasa rayukansu a rikicin Fulani makiyaya da mazauna garuruwan kudancin Kaduna.
Ko da yake wani limamin coci a yankin yace sama da mutane 800 ne suka rasa rayukansu a rikicin yankin inda hukumar ‘yan sandan jihar suka musanta hakan sannan sukayi kira ga shugabannin al’umma da su yi taka tsantsan da yadda suke fadin maganganu musamman idan basu tabbatar da sahihancin abin da za su ce ba.