Muna tattaunawa da Boko Haram akan sauran ‘Yan matan Chibok – Inji Lai Mohammed

0

Ministan watsa labarai Lai Mohammed yace lallai suna tattaunawa da kungiyar Boko Haram akan yadda sauran ‘yan matan Chibok za su dawo ga iyayensu.

Ministan ya fadi hakanne a filin jirgin saman sojin sama dake jihar Adamawa bayan sun dawo daga wata shawagi da suka je dajin Sambisa.

Lai Mohammed yace gwamnati na iyakan kokarinta wajen ganin ta kwato sauran ‘yan matan da suka rage a hannun kungiyar Boko Haram din.

Ya kara da cewa gwamnati na cigaba da tattaunawan duk da yake suna samun dan matsaloli amma duk da haka komai dai yana tafiya yadda ya kamata.

Shugabannin kungiyar BBOG ne da wadansu ‘yan jarida suka bi tawagar gwamnatin zuwa dajin Sambisa.

Share.

game da Author