Ministan Kasashen Waje, Ministan Kudi, Ministan Kasuwanci da Kasa duk sun ajiya ayyukansu a kasar Gambiya ganin yadda shugaban kasar Yahya Jammeh ya kikace akan bazai sauka daga kujeransa na shugabancin kasar Gambiya din ba.
Haka kuma gwamnan garin Banjul ya ajiye aikin nasa shima. Dukkansu dai sun fice daga kasar.
Mutanen kasar Gambiya dai suna cikin zaman dar dar ganin yadda shugaban kasar Yahya Jammeh ya da ge akan bazai sauka daga kujeran mulkin kasar ba.
Har yanzu dai Shugaban kasar Yahya Jammeh na samun matsi daga kungiyoyin AU da ECOWAS akan ya amince da sakamakon zaben da aka yi a watan Disemban 2016 kuma ya mika wa Adama Barrow mulkin kasar wanda shine ya lashe zaben.