Matakan da za’a bi domin shawo kan Cuttar da ake kamuwa dashi a dalilin kiba
1 – Iyaye su hana ‘ya’yansu cin abinci da daddare gab za suyi barci. Aba yara abinci tun da dan sauran lokaci kafin barci ya zo.
2 – Inganta abincin yara da abubuwan gina jiki da ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa.
3 – A koya ma yara yadda ake motsa jiki domin samun lafiya a makaranta da gida.
A wata bincike da hukumar Kididdiga ta kasa tayi (NBS) a 2015 ya nuna cewa kashi 1.6 bisa 100 na yara kanane suke dauke da matsalar cutar da kiba yake kawowa.
Yawan kiba yana kawo cututtuka kamar su hawan jinni, Buguwar Zuciya wanda hakan yakan sa yara su rasa rayukansu tun suna kanana.
Bayan haka kuma bincike ya nuna cewa matsalar kiba na kara yaduwa domin a yanzu cikin kashi 37 bisa 100 na mutanen da ke fama da kiba kashi 7 daga ciki yara ne inda lissafi ya nuna cewa a shekara ta 2020 yara miliyan 60 ake tsamanin za su kamu da cututtuka irin wanda yawan kiba ke kawo wa.
A kasa Najeriya bincike ya nuna cewa jihar Bayelsa tafi kowani jiha yawan yara kanana da suke da kiba
Ga yadda sakamakon binciken ya nuna:
Jihar Bayelsa kasha 2.9 bisa 100, jihar Nasarawa da kashi 2.4 bisa 100, jihar Taraba na da kashi 2.4 bisa 100.
Jihohin Borno, Anambra da Yobe basu da wannan matsalar.
Babbar likita, Teniola Taiwo-Ojo ta ce idan ba a yi hankali ba nan gaba matsalar kiba zai yi yawa a kasa Najeriya domin mun shiga cikin zamanin da yara na girma fiye da shekarunsu.
Ta ce kamata ya yi yara na girma daidai da shekarunsa misali dan shekara daya ya kamata mauyinsa ya kai kilo 10 amma idan nauyinsa ya wuce haka ta akwai matsala.
Bayanan binciken ya nuna cewa ‘ya’yan attajirai ne suka fi fama da matsalar kiba domin mafiyawan iyayen su basu kulawa da irin abincin da ‘ya’yansu ba.
Tolu Omodunbi ma’aikaciyar asibitin ikilisiyar katolika dake garin Ibadan ta ce a babban matsalar da ake fama dashi musamman a yara shine na rashin ciyar dasu abincin da ya kamata musamman ‘ya’yan talakawa.