Lokaci yayi kowa ya san abin da ake kasafta wa majalisar tarayya –Inji Ali Ndume

5

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume yace yanzu lokaci yayi da majalisar za ta bayyana ma Sanatoci da mutanen Najeriya abinda ake kasafta wa majalisar a kasafin kasa.

Yace an dade ana ta boye boye akan hakan kuma babu wani wanda ya ce komai akai.

Ndume ya kara da cewa hatta su yan majalisan basu san nawa ne majalisar ta ke samu ko kuma ta ke kashewa.

Yace bayan kudin adunkule da ake ware wa majalisar wanda ya kai naira biliyan 115 babu wanda ya san yadda ake kasafta shi.

Shugaban Majalisar dattijai da kakakin Majalisar Wakilai ne kawai suka san yadda suke kasafta kudin.

Ndume yace babu abinda zai sa ace dole sai hakan za’aci gaba da yi.

Ya kara da cewa dole ne kuma fannin zartaswa ta bada bayanai akan kasafin kudin bana saboda su san abin da za’ayi dasu da inda za’a kashesu.

Yace naira biliyan 40 da aka ware ma yankin Arewa maso gabas yayi kadan.

Share.

game da Author