Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ba zai yi aiki da sakamakon binciken da majalisar dattijai ta aika masa dashi ba wanda ta shawarce shi da ya kori Sakataren gwamnatin Tarayya David Babachir akan kwangilar cire ciyawa a kogin Yobe.
Buhari yace kwamitin da suka binciki kwangilar cire ciyawar basuyi ma Babachir adalci ba domin basu gaiyaceshi domin ya zo gabanta ya kare kanshi ba.
Yace kamar yadda rahoton ya nuna, mutane 3 ne kawai suka sanya hannu akan sakamakon binciken mai makon sanatoci 9 da aka nada su binciki kwangilan.
Buhari yace adalilin hakan bai gamsu da wannan sakamakon bicike ba kuma ba zai yi amfani da shi wajen dakatarwa ko koran Sakataren gwamnatin tarayya din ba.
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya karanta wasikar shugaban kasan a zauren majalisar yau.