Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya kuma shugaban kwamitin majalisar dattijan da suka binciki zargin yin almundahana da kudaden da sakataren gwamnatin tarayya David Babchir yayi kwangilar cire ciyawa a jihar Yobe yace ba daidai bane dalilan shugaban Kasa ya bada akan wai sune ya sa ba zai dauki mataki akan sakamakon binciken majalisar ba.
A martanin da ya maida jim kadan bayan shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya karanta wasikar shugaban kasa kan hakan, Shehu Sani ya mike domin musanta abubuwan da shugaban kasa yace ya dogara dasu a matsayin hujjojin sa na kin amfani da sakamakon binciken nasu.
Shehu Sani yace ba daidai bane cewa da Buhari yayi wai mutane 3 ne kawai suka sa hannu a sakamakon binciken. Yace sanatoci 7 ne cikin 9 suka sa hannu sannan yace ba kamar yadda shugaban kasa yace wai ba’a gaiyaci sakataren gwamnatin tarayya domin ya kare kansa ba, Sanata Shehu Sani yace bayan wasika da kwamitin suka tura ma shi Babachir din sun sanar a gidajen jaridu 3 domin kowa ya san da zaman.
Yace ofishin sakataren gwamnatin tarayya din sun aika masa da takardan amsa sakon kwamitin.
Yace da gwamnati ke bin alkalai an yi amfani da matakai tsaurara amma gashi yanzu da yake wannan na fadar shugaban kasa ne ana bi da lalama.