Mataimakin sashen kimiya da fasaha da sadarwa ta cibiyar NCDC Lawal Bakare yace a shekarar bara jihohi 7 ne suka koka da kamuwa da zazabin cutar Lasa wanda ya janyo mutuwar mutane 19 a wasu jihohin kasannan.
“Saboda haka ne ya sa hukumar ta kara dagewa domin ta dakatar dayaduwar cutar.”
Ya yi bayanin cewa a shekarar bara cibiyar ta fara aiwatar da shirye-shiriyen ta na kawar da cutar wanda zai kai har zuwa tsakiyar wannan shekaran.
Ya kuma ce cibiyar za ta hada kai da jihohin da mutanenta suka kamu da cutar ta hanyar kara fadakar da malaman asibitocin yadda zasu taimaka wa mara sa lafiyan, samar da magungunar da za su bukata, gwajin mutane da kuma nemo hanyoyin da zai taimaka wurin dakile yaduwar cutar.
Bakare yace ana warkewa daga cutar zazabin lasa idan an kawo mara lafiya da wuri, inda rashin yin hakan ya kan sa majinyaci ya rasa ransa.
Bayan haka ya kara jaddada mahimancin fadakar da mutane akan cutar kuma ya shawarci jama’a da su tsaftace muhallin su ta hanyar kange abincin su daga beraye ko kuma fitsarin sa wanda shine ya ke sa a kamu da cutar.