Babban Kotun tarrayya da ke zamanta a Abuja ta sake tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Sambo Dasuki a shekarar 2015 na sake shi.
Alkalin Kotun mai shari’a Baba Yusuf yace Dasuki ya cancanci a bashi beli kamar yadda kotun ECOWAS ta yanke a wancan lokacin kuma shima ya tabbatar da hakan.
Wani Babban Lauya da ya halarci zaman yau yace hukumar SSS ba ta da wani abin da za ta iya cewa musamman ganin yadda Kotunan suke ta yanke hukunci iri daya akan Sambo Dasuki.
“Ya kamata ace ya dade ya na more belin sa amma har yanzu anki a sake shi.”
Yayi kira ga hukumar SSS da ta bi umarnin kotu akan hakan musamman ganin cewa hakan bai saba ma doka ba sai dai kin bin hukuncin kotun zai zama laifi.
Ana daure da Ibrahim Dasuki ne da wadansu su 5 akan tuhumarsa da akeyi na waskewa da kudaden siyan makamai a lokacin mulkin Jonathan Goodluck daya kai dala biliyan 2.
Dasuki ya musanta hakan a kotu.
An daga karan zuwa watan Fabrairu mai zuwa.