Tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ken Nnamani ya canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Da yake sanar ma wamnnan gidan jarida, PREMIUM TIMES, Nnamani yace makasudin canza shekarsa shine kira da mutanen yankinsa suke tayi akansa da ya koma jam’iyyar APC domin samo musu cigaban da ya kamata.
Yace shi na jama’a ne kuma jama’ane suka kawo masa kukansu saboda haka dole ya amsa.
Daga karshe ya koka da yadda jam’iyyar sa ta da wato PDP ta zama a cikin dalilan da ya sa ya canza shekan zuwa jam’iyyar APC.