Hukumar Kididdiga ta kasa (NBS) ta ce sama da kashi 89 bisa 100 na ‘yan Najeriya basu da rijista a shirin fansho na kasa.
Hukumar ta yi bayanin cewa a shekarar bara kashi 10.8 ne kawai daga cikin adadin ma’aikatan Najeriya ke da rijistan fansho domin mafi yawan ma’aikata manoma ne wanda daga ciki maza na da kashi 14 bisa 100 sanan mata na da kashi 6 bisa 100.
Hakanan kuma idan aka kwatanta adadin yawan maza da mata wadanda suke da rijistan fansho za a ga cewa maza sun fi yawa domin maza na da kashi 71.13 bisa 100 sannan mata na da kashi 28.87 bisa 100.
Bincike ya nuna cewa ma’aikatu masu zaman kansu sun fi yawan ma’aikata da suke da rijista shirin fansho ta kasa.