Kasar Saudiyya ta dawo ma Najeriya yawan kujeran maniyyata aikin Hajji da ta rage a Hajjin bara.
A shekaran da ya gabata kasar ta rage ma Najeriya yawan kujerun maniyyatan kasar daga 95,000 zuwa 75,000 amma ta sanar da maida wa Najeriya yawan kujerun daga aikin Hajji mai zuwa.
Kungiyar masu aiko da rahotanni akan aikin haji ta kasa ne ta sanar da hakan a garin Kaduna ranar Asabar.