NASARORI
1. Kokarin da gwamnatinsa ta keyi domin samar wa Karamar Hukumar Zariya da ruwan Fanfo.
Wahalar ruwan fanfo a Karamar hukumar Zariya ya kai tsawon shekara 30 jama’ar yankin suna fama da rashinsa.
El-Rufai ya tsaya tsayin daka domin ganin ruwa ya samu a Zariya domin aiki akeyi babu kakkautawa.
2. Kasafin kudi ta shekara ta 2017.
Gwamnan Kaduna Nasir El- Rufai shine gwamna na farko da ya fara sanya wa kasafin kudin jihar hannu a wannan shekara ta 2016. Sannan da yin amfani da kwararru domin ganin an sami fayyacaccen kasafin da zai amfani mutanen Jihar.
3. Ciyar da yaran makarantun firamari.
A dalilin ciyar da yara abinci a makarantun gwamnati da ke jihar Kaduna dubban yara ne masu garari a titunan jihar suka koma makaranta domin samun ilimi tare da abincin ci.
Duk da haka gwamna El-Rufai ya gina rijiyar burtsatse, samar da kujeru da teburan karatu, gyara da gina ajijuwa da dakunan bahaya a makarantu 400 dake fadin jihar Kaduna.
4. Samar da aikin yi
El-Rufa’I a wannan shekaran ya samarda da ayyukan yi ga matasan jihar sama da 4000 wanda ya hada da aikin malanta 2000 da aikin KASTELEA 3000.
5. Gyaran titin Ahamadu Bello
Matsaloloin da gwamnan ya fuskanta.
6. Rikicin kungiyar ‘yan Shi’a.
7. Rikicin kundancin jihar Kaduna.
8. Tantance ma’aikata.
9. Ayyukan kungiyar ‘yan Shara.
10. Tafiyar hawainiya da ayyuka sukeyi a jihar.