Jarumai Maza 10 da suka yi fice a harkar fina-finan Hausa a 2016

0

A wannan shekara ta 2016 Jarumai maza a farfajiyar fina-finan hausa sun kara kaimi da hazaka a wajen shirya wa da kokari wajen kara kwazo a aikinsu.

Ga jerin jaruman maza guda 10 da suka yi fice a wannan shekaran a harkar finafinan Hausa wanda gidan jaridar PREMIUM TIMES ta tsaro bayan nazari da tayi akan finafinan da jaruman suka fito a ciki.

1. Na 1 shine ALI NUHU

Ali Nuhu wanda akafi sani da Sarki, baya mai goya marayu. Bincike ya nuna cewa Ali Nuhu yana da ga cikin wadanda suka fi fitowa a finafinai a farfajiyar finanfinan Hausa.

Yana da masoya masu binsa a shafin sa na Instagram da ya kai sama da mutane 337,000.

Ali Nuhu ne mai kamfanin shirya finafinai na FKD wanda ta gano jarumai kamarsu; Nafeesat Abdullahi, Rahama Sadau da sauran su.

Shine dan wasa na farko a farfajiyar finafinan Hausa da ya sami sa hannun kamfanin Twitter a shafinsa sannan na farko da ya kafa shafi ta farko da zaka iya kallo da aron finadfinan sa ta yanar gizo.

Ali Nuhu Malami sannan jakadar kamfanonine da yawa a kasa Najeriya.

ya fito a fina-finai masu yawa amma ga kadan da da cikin sunayen fina-finan da ya fito a cikin shekaran nan; Muradin raina, Akasi,Matar Bahaushe,Mu’amalat, Gobarar Mata da kuma sauran su.

2. Na 2 shine SADI SANI SADIQ

Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi kiranshi da Gambo a farfajiyar Kannywood ya yi nuna jarumtarsa a fim din Dan Marayana shekara ta 2013.

Sadiq ya na daga cikin dan wasan da ya ke iya hawa ko wace irin mataki ka dora shi a finafinai.

Sadiq yana da mabiya 206,000 a dandalin Instagram kuma ya fito a fina-finai masu yawan gaske amma ga sunayen fina-finan da ya fito a wannan shekarar; Mati da Lado, Hanyar Kano, Takanas na Kano,Ruma da sauran su.

3. Na 3 Shine ADAM A ZANGO

Gwanin rawa, Adam A Zango shima yayi fice a farfajiyar finafinan Hausa a wannan shekara.

Ya na da mabiya 270,000 a Instagram kuma ya fito a fina-finai kamar Basaja, Gwaska, Rabin Raina, Uzuri da kuma sauran su.

4. RABI’U RIKADAWA
5. SULEIMAN BASHO
6. NUHU ABDULAHI
7. YAKUBU MOHAMMED
8. FALALU DORAYI
9. ADO GWANJA
10. AHMAD NUHU

Share.

game da Author