Shugaban hukumar bada ilimi da samar da walwalar jama’a na jihar Katsina Ibrahim Nasir yace an tsinto jarirai 18 cikin wata 4 a garin Funtua.
Yace akan tsinto jariranne a makwararrun ruwa, Juji, kwata da gidajen da ba’a gama gininsu ba.
Ibrahim Nasiru yace abin ya zama ruwan dare a yankin domin ko a jiya 24 ga watan Janairu an tsinto wata jaririya a wata tsohuwar masai.
Yace abin fa yanzu ya zama ruwan dare a gari na Funtua.