‘Ya’yan jam’iyyar APC a majalisar dattijai ta tsige shugaban masu rinjaye na majalisar Ali Ndume sannan ta zabi Ahmad Lawal a matsayin sabon shugaban masu rinjaye a majalisar.
Yanzu dai ana jiran shugaban majalisar ne Bukola Saraki ya sanar da hakan a majalisar a zamanta na gaba.