Jami’an ‘yansandan sirri sun kawo wata samame kamfanin jaridar PREMIUM TIMES in da suka kama mawallafin gidan jaridar Dapo Olorunyomi da Evelyn Okakwu, mai kawo ma gidan jaridar rahotanni akan Kotu.
Jami’an dai sunce wai an turo su ne su zo su kama shugaban kamfanin da Evelyn Okakwu umurni da ga ofishin Hafsan sojojin Najeriya saboda yadda suke tsaga gaskiya a labaran su.