Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam JNI ta ce ba za ta sa ido ta bari ana ci wa musulunci da musulmai fuska ba da sunan addini akan rikicin kudancin Kaduna ba.
Sakataren kungiyar Dr Aliyu khalid a wata takarda ta musamman yace wadansu malaman Majami’an kiristoci a yankin kudancin Kadunan sun mai da rikicin yankin siyasa.
Yace suna kirkiro lambobi su ce wai yawan mutanen da aka kasha Kenan a yankin a rikicin mazauna kauyukan garuruwan da Fulani.
Yace su sani cewa abin da ya faru da musulman yankin a rikicin 2011 ba’a manta da shi ba.
Yace mai makon shugabannin addinin su nemi hada kan jama’a domin asami zaman lafiya kokari sukeyi su ruruta abin da karerayi.
Kungiyar Jama’atu din ta jinjina ma hukumar tsaron jihar Kaduna da gwamnan jihar akan irin yadda suka nuna jarumtarsu da kwarewa duk da irin wulakancin da gwamnan ya sha a yankin domin ganin an kawo karshen ire-iren wadannan tashin hankali a jihar baki daya.