Rahoton kwamitin da gwamnan Jihar BAUCHI Mohammed Abubakar ya nada domin binciken sama da fadi da kudaden jihar da tsohon gwamnan Isa Yuguda yayi kwamitin ya gano wasu boyayyun almundahana da wawushe kudin jihar da Yuguda yayi.
Binciken ya nuna yadda tsohon gwamnan ya kakkara kudaden kwangiloli sannan ya biya dayawa daga cikinsu ba tare da anyi aikin ba.
Wasu kuma daga cikin ayyukan an gano cewa anyi su ne zuwa rabi amma kuma an biya kudaden aikin cas.
Bayan haka kuma binciken ya nuna yadda Yuguda da wasu da ga cikin kwamishinoninsa musamman na kananan hukumomi suka dinga watanda da kudaden kananan hukumomin jihar domin San ransu kawai.
Kwamitin ta bada shawaran da a gurfanar da tsohon gwamnan Isa Yuguda domin ya zo yayi bayani akan bacewar wadannan makudan kudade.