Babban sakataren hukumar NPHCDA Faisal Shuaibu ya shawarci shugabanin kasuwa da kuma kwarraru da su rungumi shirye-shiryen da gwamnatin Buhari ta kirkiro domin gyara cibiyoyin kiwon lafiya a kasa Najeriya.
“Hakan zai sa mutane musamman ‘yan karkara su sami ingantarciyar kiwon lafiya.”
Ya kuma shawarci shugabanin kananan hukumomi da gwamnonin jihohi da su yi koyi da abin da gwamnatin tarayya ta ke yi domin samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.
Faisal Shuaibu ya yi aiki da gidauniyar Linda da Bill Gates a kasar Amurika kafin ya zama shugaban hukumar NPHCDA.
Bayan haka ya shawarci ma’aikatan hukumarsa da kuma malaman asibiti da su yi aiki tukuru sannan su nisantarda kansu daga cin hanci da rashawa.