Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya ta ce kasa Najeriya ita ce ta fi ko wani kasa yawan matan da ake yi ma kaciya domin bayanai sun nuna cewa mata da ‘yan matan da aka yi musu kaciya sun kai miliyan 40.
Wata mazauniyan jihar Legas Rosaline Nkwo mai shekara 57 ta ce a dalilin wannan mummunar al’adar gargajiya ce ya sa aurenta guda biyu suka lalace.
Ta ce mahaifiyarta ta fada mata cewa tana shekara biyu lokacin da aka yi mata kaciyan. Ko da Rosaline ta girma, maza gudun ta suke yi idan sun kusance ta hakan ya sa ta cikin wani halin kunci, fushi, kadaici, rashin moriya, tabuwan hankali da kuma sauran su.
Ta ce abin da ya fi damin ta shine rashin kudi da ta ke ciki domin ta sami lafiya. Rasaline kamar sauran mata da ‘yan matan Najeriya suka yi bayanin yarda wannan mummunan ala’dan gargajiyan ta saka su cikin wani hali.
Abin mamaki shine a kasar Najeriya duk addinai guda biyu da mutane ke bi a kasar kamar yadda masana suka sanar bayan wata bincike da suka gudanar ya nuna cewa inda addinan suka yarda ‘Musulunci ko Kirsta’ da wannan al’adan.
Duk da haka kuma gwamnati ta yi iya kan kokarinta domin kirkirowa da kafa dokar da zai hana yi wa mata kaciya a shekarar 2015 amma hakan bai sa an dai na ba.
Jihohi kamar su Legas, Ondo, Osun, Ekiti, Bayelsa, Edo, Cross rivers suna kokarin ganin wannan abu bai ciga ba da aukuwa.
Abin tambaya shine shin mene wannan kaciyar matan kuma mene anfanin ta?
Wata ma’aikaciyar hukumar dinkin duniya ta ce kaciyan mace shine yanke wani tarin fata da ke gaban mace wanda aka fi sani da turance ‘clitoris’ domin a hana mace ko ‘yan mata zama Kharijai
kuma a shirya su domin zaman aure.
Ta ce wannan al’adan ya fi yawa a ta yankin kudu maso yamma duk da cewa mutanen yankin suna da wayewa tunda dadewa.
domin wata bincike ya gano cewa a jihar Osun adadin matan da aka yi musu kaciya ya kai kashi 76.3 bisa 100, a jihar Ekiti kuwa ya kai kashi 71.2, Oyo kashi 69.7, Ebonyi 55.6, Imo 48.8, Legas 44.8.
Mr Oyefunsho Orenugu dan kwamitin da suke shirye-shirye aka kaciyan mata na kasashen Afrika da sauran manyan likitocin Najeriya sunyi bayani akan illolin yi wa mata kaciya kamar haka;
1. Fushi
2. Tabuwan hankali
3. Rashin son saduwa da Namiji
4. Yakan kawo wahala wurin haihuwa
5. Yoyon fitsari ga ‘Ya mace
6. Mata kan kamu da wasu cuttutuka a gabansu
7. Zubar jini da har ya kan kai ga mutuwa
8. Samun matsala wurin yin fitsari da kuma sauran su.
Bayan haka wani babban likitan kwakwalwa Nathaniel Ayodeji tare da wasu manyan likitoci sunce ce yakamata ayi kokarin ganin an shawo kan wannan matsalar.
Sun ba da shawara kamar haka:
1. Matan da aka yi musu kaciya da matan da ba a yi musu kaciyan ba su yi kokarin fitowa su fada wa duniya illar yi wa mata kaciya domin su zama kamar murya ga sauran mata da suke cikin irin wanan matsalar.
2. Likitoci za su iya taimakawa da shawara ga matan domin su zama abin moriya wa ‘yan uwa da kuma kasar.
3. A fadakar da mutane da ‘yan makaranta illar yi wa mata kaciya a makarantu, asibitoci, wuraren ibada da kuma sauransu.
4. Likitoci su yi kokarin hada wata kungiya na matan da aka yi masu kaciya domin matan su fadi yadda yake musu da illarta sannan domin gano yadda za a iya taimaka masu.
5. Gwamnati ta iya kirkiro da dokokin da za su hana wannan al’adan da kuma hukunta duk wanda aka sa mu suna yin hakan.
Idan mutanen kasar Najeriya suka hada karfi da karfe, za a iya cimma burin kawar da yi wa mata kaciya a kasar da kuma duniya gaba daya.