Hukumar NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi a jihar Legas

0

A ranar Alhamis ne hukumar NDLEA ta ce ta kama mugayen kwayoyi a hannun wasu masu safararsu a jihar Legas.

Hukumar ta ce ta kama kwayoyi kamar su; Cannabis wato wata ganye ce ce da take da sunadarin sa maye da ya kai kilo 16,327.398, kwayan tramadol kilo 192.918, hodar ibilis kilo 121, tabar wiwi 37, kwayar Diazepan kilo 46.7 da kuma kwayar Rophenol.

Hukumar ta ce tana aiki tukuru domin ganin ta hana safarar kwayoyin sannan ta jinjina wa ma’aikatanta saboda kwazon da suke nunawa domin gani an rage irin wadannan ayyuka musamman ga matasan jihar.

A shekaran 2015, hukumar ta kama mutane 362 dake amfani da irin wadannan kwayoyi, ta kuma kama kwayoyi da ya kai kilo 12,127.73 kuma sun gurfanar da mutane sama da 50 wanda suke shigowa da kwayoyi kasa Najeriya.

Shugaban hukumar NDLEA Muhammed Abdullahi ya ce ya zama dole dukufa wajen yin yaki da shayeshaye da kuma shigowa da miyagun kwayoyi a kasa Najeriya da kuma jihar musamman yadda manyan mutanen da ke sawa a shigo da miyagun kwayoyin ke fakon jihar Legas domin yawan tashoshin jiragen sama da na ruwa da kuma yawan kasuwanin da ke jihar.

Share.

game da Author