Hanyoyin da Mata za su bi domin kare kansu daga kamuwa da cutar dajin mahaifa

0

Kungiyar kula da kiwon lafiyar Jama’a tare hadin kan cibiyar samar da bayanai akan abubuwan da ke sa mata su kamu da ciwon daji.

Kungiyar tace mata su yi kokarin yin gwaji domin ganowa ko suna dauke da cutar dajin da yake tsirowa a kusa da maihafarsu.

Hukumar ta ba da shawaran ne a lokacin da ta takai ziyara wata kungiyar addini ta mata a garin Abule-Ijoko jihar Ogun.

A yayin ziyarar ta yi bayanin cewa adadin matan da ke dauke da cutar ya kai 14,089 a kasar Najeriya kuma a kowani shekara mata 8,240 ke mutuwa daga cutar.

Wannan shine dalilin da ya sa hukumar take fadakar da mata game da cutar.

Bayan haka babban darekta a hukumar, Folasade Ofurune ta yi kira ga mata da su dinga kokarin zuwa asibiti domin yin gwaji akan cutar saboda irin nuna rashin sanin tutar da illarta da mata suka nuna.da mata da yawa sun nuna mamaki da kuma rashin sanin su game da cutar.

Hanyoyin da za a iya bi domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

1. Mata za su iya karban rigakafin cutar wato HPV vaccine Kenan da turance tun suna shekara 11 ko kuma kamin mace ta fara saduwa da Namiji

2. Iyaye su yi kokarin yi wa ya’yansu mata da maza rigakafin domin madance sauran cuttutukar da daga daji ke kawowa.

3. Fadakar da mutane akan cutar domin kara inganta kiwon lafiyar mutanen duniya gaba daya.

Malama Ofurune ta ce hukumar za ta cigaba da fadakar da mata da kuma yi musu gwaji a sauran garurukan Najerya a shekara mai zuwa domin bincike ya nuna cewa cutar ya fi kama mata‘yan shekara 16 zuwa 60 musamman a kasashen kudu da Saharan Afirka.

Ta ce a duniya gaba daya cutar ne na biyu da ya ke kisar mata domin a kowani minti biyu mata na mutuwa da ga cutar dajin.

Daga karshe Malaman Ofurune ta ce yin gwajin cutar ba tsada saboda akwai ingantantun naurorin da suke gano cutar da wuri kuma tana tabbatar wa mutane cewa gwajin zai cigaba domin kawancentar da suka hada da kungiyar da take zaman kanta wato ‘Society for Familiy Health’ domin samar da gwaji ingantacce.

Share.

game da Author