Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da cibiyar kiwon lafiya a garin Kuchigoro da ke Abuja

0

Kamar yadda ta sanar cewa za a gyara da wadata akalla cibiyar kiwon lafiya daya a kowani kauye a kasa Najeriya, ma’aikatan kiwon lafiya ta kaddamar da cibiya ta farko a kauyen Kuchigoro dake garin Abuja.

Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adebowale ya kara da cewa gwamnati ta gama shiri domin ganin kowace kauye a Kasa Najeriya ta samu akalla cibiyan kiwon lafiya guda daya da yake aiki.

Ya ce ko wace cibiya za’a wadata ta da magunguna da kayan aiki domin mutanen wannan yaki.

Isaac Adebowale ya fadi hakanne a wajen kaddamar da cibiyar kiwon lafiya na Kuchigoro dake garin Abuja.

Share.

game da Author