Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna Andrew Nok yace gwamnatin jihar ta kashe sama da biliyan 8 a cikin wata 8 domin ciyar da daliban makarantu a jihar.
Kwamishinan ya fadi hakanne a makarantar sakandaren mata na Sarauniya Amina da ke garin Kaduna.
Yace gwamnatin El-Rufai zata daukaka darajar makarantun sakandare 15 a jihar da suka hada da Makarantar Sakandare na Rimi, da makarantun Sakandaren gwamnati da ke Saminaka, Kwoi, da dai sauransu.
Kwamishina Nok yace gwamnati ta kashe miliyan 600 domin gyara gyare a makarantar Sarauniya Amina da ke Kaduna.
Ya fadi hakanne a wajen kaddamar da sabon dakin karatu na zamani a makarantar.