Gwamnatin jihar Bauchi ta maida wa iyayen wasu almajirai 176 ‘ya’yansu da suka fito da ga kananan hukumomin jihar.
Kwamishinan wasanni da matasa na jihar Zubairu Madaki yace gwamnatin jihar Filato ne suka kawo musu Almajiran cewa sun kama su a a hanyarsu ta zuwa garin Jagindi da ke jihar Kaduna domin yin bara.
Yace jami’an tsaro sun dauka barayin yara ne suka sato su, kafin daga baya suka gane cewa Almajirai ne zasu bara.
Almajira 24 ‘yan karamar hukumar Dambam ne, Ganjuwa da Ningi suna da 20 kowanne, Alkeleri na da 4, sannan Misau, Bauchi da Gamawa suna da daya daya.
Yace Jihar Katsina na da Almajirai 16 cikinsu sannan Kaduna na da 14.
Malamin su Ibrahim Yayaji ya gaya wa jami’an tsaro cewa zai kanshi Jagindi ne domin yin sana’ar Almajiranci.
Discussion about this post