Shugaban kula da cibiyoyin kiwon lafiya na Kasa mai rikon kwarya Emmanuel Odu yace gwamnati tare da hadin gwiwar hukumar da ke kula da gyara cibiyoyin kiwon lafiya na kasa na iya kan kokarinta domin sharewa ‘yan Najeriya hawayen su na rashin samun ingatantacciyar kiwon lafiya ta hanyar ganin cewa an gyra sannan an wadata a kalla cibiya guda daya a kowani mazabar dan majalisar dattijai dake fadin kasar nan.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole shima yace tabas wannan yana daya daga cikin kyawawan ayyukan da wannan gwamnati ke shirin yi wanda zai taimaka wa mutane wajen samun ingattaccen kiwon lafiya.
Mr Odu ya yi bayanin cewa a kowace mazabar dan majalisar dattijai sun zabo cibiyan kiwon lafiya guda daya wanda za su gyara.
Ya kuma ce inganta cibiyoyin zai taimaka wurin kawar da cututtuka kamar su ciwon sanyi, cutar kanjamau, rage mutuwar uwaye da ‘ya’yansu, da kuma gyara hanyoyin da akeyin alluran rigakafi a kasar gaba daya.