Gwamnati ta kona dandazon jabun magunguna a jihar Ribas

1

A ranar Laraba ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya jagoranci kona dandazon jabun magunguna wanda yakai naira biliyan 9 a jihar Ribas.

Bincike ya nuna cewa hadin gwiwar da hukumomin NAFDAC, Kwastom da kuma na NDLEA suka yi ne ya sa aka sami nasaran wannan babbar kamun wanda rabon da ayi hakan ya kai shekara sama da 25.

Ministan ya shawarci malaman asibiti da su sa ido wajen ganin marasa lafiya suna samun magunguna masu kyau kuma ingantattu ta hanyar aiki da masu safaran magungunan wajen tantance sahihai daga cikinsu wanda hakan zai sa a samu raguwan tsadar magungunan kuma ya kashe kasuwannin Jabu daga cikinsu.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiyar jihar Rivers Theophilus Adagma da shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar jihar Chike Okafor sun yaba da abin da hukumomin suka yi kuma sun yi alkawarin mara wa gwamnati baya domin kawar da sayar da jabun magunguna a kasa Najeriya.

Shugaban hukumar kwastom Hammed Ali wanda mataimakinsa Sanusi Umar ya wakilce shi yace tabas hukumarsa ta dade da ta yi irin wannan kamun kuma yace za’a cigaba da samun irin wadannan nasarori ne idan hukumomin da hakkin hakan ya rataya a kansu sun hada karfi da karfe domin kawar da irin wannan munanan ayukka.

Shugaban hukumar NAFDAC Yetunde Oni ta shawarci ‘yan Najeriya da su mara wa hukumar baya akan yaki da takeyi domin kawar da jabun magunguna a kasa Najeriya. Ta kuma shawarci masu shigo da magunguna daga kasashen waje da su tabbatar da amincin magungunan kafin su shigo da su Najeriya.

Share.

game da Author