Kwamishinan Shari’ar jihar Borno Kaka Shehu Lawan yace jami’an tsaron jihar sun gano wani wuri da ake siyar da jarirai a jihar.
Ya kara da cewa an kama wadansu mata su 4 da wani mutumi da yake da mallakin gidan.
Yanzu haka dai suna tsare a kurkukun jihar kafin fuskantar shari’a.
Bayan haka kuma gwamnatin jihar ta hana siyar da giya da rufe gidajen Karuwai a jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa akwai wadansu shaguna a wasu unguwanni a jihar da gwamnati ta tashe su domin kau da cinkoso a wuraren da kuma mazauna unguwan.
Ta ce tayi hakanne sabod ta kau da duk wani maboya da Boko Haram zasu iya amfani dasu a jihar.
Gwamnati ta umurcesu da sukoma wasu kasuwanni a jihar.