Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya yi kira ga kungiyar neman dawowa da ‘yan matan Chibok (BBOG) wato Bring Back Our Girls cewa gwamnati ba makiyansu bane kuma ta na tare dasu musamman akan maganar ‘yan matan Chibok.
Lai Mohammed ya ce furicin da kungiyar ta keyi na batanci akan gwamnati bai dace.
Yace dalilin haka ne ya sa gwamnati ta gayyaci wakilan kungiyar domin su bisu dajin Sambisa su gani ma idanuwarsu irin kokarin da gwamnati ta keyi wajen ganin ta dawo da yan matan Chibok ga iyayensu, sai dai duk da haka yau gashi an wayi gari kungiyar na zargin gwamnatin da nuna halin ko in kula akan maganar dawowa da ‘yan matan Chibok din.
A dalilin haka ne yasa ministan ya shawarci kungiyar da su iya ma bakinsu sannan su yi ma gwamnati adalci akan aubuwan da za su rinka fadi nan gaba kada garin ne man kiba su samo rama.
Daga karshe ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su karaya akan kokarin da gwamnati takeyi na ganin ta dawo da ‘yan matan Chibok domin lokacin da Boko Haram ta kama ‘yan matan babu wanda ya zata zasu dawo.
Ya kuma ce gwamnati za ta cigaba da kokarin da take yi a yanzu hakan duk da korafe-korafen da take samu akan kokarin dawo da ‘yan matan Chibok din.