‘Yar wasan finafinan Hausa Rahama Sadau ta koka da yadda ma’aikatan filin jirgin saman Kaduna suka wulakanta a filin.
Da ta ke bayanin hakan a shafin sadarwan ta na twitter tace ma’aikatan basu san aikinsu ba sannan jahilai ne.
Ta ce sun bata ma rai matuka sannan ta yi ikirarin ba za ta sake hawa jirgi ta filin jirgin saman Kaduna ba.
Ta kara da cewa filin ya fi ko wani filin jirgi muni a kasa sannan ma’aikatanta basu da horo akan yadda zasu kula da mutane.