Wani farfesan kuma likitan dabbobi Aliyu Mani da wadansu su mutane 4 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar tashin bam a wani masallaci da ke jami’ar Maiduguri
Bam har guda 2 ne su ka fashe a wani masallaci da kofar shiga jami’ar Maiduguri da safiyar litinin dinnan.
Bam din dai ya tashi ne a lokacin sallar Asuba.
Hukumar yasandan jihar tace jami’anta da suke kofar makarantar sun harbe wata yarinya year shekara 12 a lokacin da take kokarin ta da bam din da me daure a jikinta.
Mutane 4 bayan farfesa Mani suka rasa rayukansu inda wata mazauniyar jami’an ta ce mahaifinta ya fice kenan daga masallacin kafin Bam din ya tashi.
Ta ce mutane da yawa da ke cikin masallacin a wannan lokaci duk sun rasa rayukansu.
Bam na biyu kuma ya tashi ne a kofar shiga Jami’ar amma yarinyar da ta ke dauke dashi ne kawai ta rasa ranta.
Koda yake babu wata kungiya da tace itace ta aikata hakan, ana ganin kungiyar Boko Haram ne suka aikata wannan mummunar aikin.
An kwashe gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu inda kuma aka kai wadanda suka samu raunuka su 17 asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri din.