El-Rufai ya nada shugabannin ma’aikatu mallakar jihar Kaduna 3

1

Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai ya nada sababbin shugabannin ma’aikatun jihar Kaduna guda 3.

Wadanda aka nada sun hada da Bashir Umaru Lere, (Wamban Lere) a matsayin shugaban hukumar Wadata ruwan sha a karkara da safta wato (RUWASSA), Dominic Bincike Dogo, Shugaban hukumar samar da walwala da cigaban al’umma CSDA) da Eng. Ibrahim Mua’zu, shugaban hukumar ayyuka, (KAPWA)

Kakakin gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka yau litini a garin Kaduna.

Gwamna El-Rufai ya yi kira ga wadanda aka nada da su ba mara da kunya wajen yin aiki tukuru da ganin an cimma nasara akan abin da gwamnatin ta sa a gaba.

Share.

game da Author