Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki yace tsige Ali Ndume da majalisar tayi duk cikin aiki ne amma babu wani abu bayan hakan.
Saraki ya fadi hakanne a fadar shugaban kasa bayan wata ganawan sirri da yayi da Buhari.
Yace babu wani mutum daya da ya fi karfin majalisar saboda haka za’a iya canji duk lokacin da ake ganin ya kamata kuma akan kowa.
Majalisar dai ta tsige Ali Ndume ne bayan ‘ya’yan jam’iyyar APC a majalisar sun nuna goyon bayan hakan.