Shugaban kamfanonin Dangote, Aliko Dangote yace dole ne jihar Kano da Kaduna su ba da bayanai akan kudaden da aka tallafi musu da shi domin yin amfani dasu wajen kawo karshen cutar Polio a jihohinsu.
Dangote yace Gidauniyar sa na Dangote da Bill and Melinda sun ba jihohin kudade masu dinbin yawa domin taimaka ma jihohin wajen yaki da cutar Polio.
Dangote ya yaba ma gwamnonin jihohin biyu akan yadda suka nuna jarumtarsu domin ganin sun kirkiro manufofi masu amfani domin cigaban al’ummar jihohinsu.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da yake nashi jawabin a taron yace jihar Kaduna tayi rawar gani musamman a fannin samar wa mutanen jihar da kiwon lafiya na gari.
Ya kara da cewa jihar za ta bada bayanai akan abubuwan da tayi da nata kudaden.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya nuna farin cikinsa akan kokarin da gidauniyar dangote takeyi musamman wajen ganin ta taimakawa jihohi domin kawo karshe cutar Polio a kasa Najeriya.
Ya kuma ce zasu cigaba da wayar wa mutanen jihar akai domin fahimtar anfanin da ke cikin yin rigakafi ga ‘ya’yansu.