Dan wasa Riyad Mahrez ne ya lashe kyautar gwarzon shekara na nahiyar Afirka na 2016

1

Dan wasan kwallon Kafa na kasar Algeriya Riyad Mahrez wanda ya ke buga kwallon sa na kwararru a kungiyar kwallon kafa na Leicester City dake kasar Ingila ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na nahiyar Afrika na 2016.

A watan Disambar da ya gabata, Dan wasa Riyad Mahrez ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka na BBC na 2016.

A sashen mata kuwa, ‘yar Najeriya Asisat Oshoala ce ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasan kwallon kafa ta Afirka ta 2016 ta CAF.

An gudanar da bikin raba kyautukan ne a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Share.

game da Author