Hashiru Aminu dan asalin jihar Katsina kuma babban ma’aikacine a kamfinin CISCO.
A wata hira ta musamman da yayi da gidan jaridar PREMIUM TIMES ya fada mana yadda masu son su sami irin wadannan shaida da ya samu a aikin Networking za su yi domin cimma burinsu.
Da muka tambayeshi daya daga cikin abubuwan da mutum zai sa agaba tun da wuri yace “ Karatu da son yin abinda aka sa agaba shine mabudin nasarar da ya samu.”
Yace karatun Networking Karatune da yake neman mutum ya dage da karatu sannan ya yi kokarin ganin duk abin da yake so domin samun nasara a karatunsa ya samu.
Yace ko da yake akwai dan tsada amma ya na ba wadanda suke son yin irin karatun nasa da su mai da hankali domin ganin sun sami nasara akai.
Hashiru shine dan Najeriya na frako sanan dan Afrika ta yamma na farko sannan na biyu a nahiyar Afrika da ya sa mi nasara a irin wannan jarabawa.