Cutar kazuwa ya kama fursunoni a jihar Gombe

0

Babban jami’in kiwon lafiya na jihar Gombe Joshua Abubakar ya ce kusan sa ma da kasha 50 na fursunonin jihar suna fama da cutar kazuwa.

Cutar kazuwa wata cuta ce da ke kama fatar mutum wanda rashin tsafta ke kawo shi sannan hanya daya da ake gane cutar ta kama jikin mutum shine za’a ga ya na ta susa da kuma fitowar kuraje a gabobin sa.

Ya kuma ce anfi kamuwa da cutar a makarantun kwanan bodin da kuma gidan yari.

Kwamishinan aiyukkan jihar Usman Ribadu bayan ya ba da gudumnawar magunguna da kayayyakin tsaftace muhalli ya kuma shawarci mazauna gidan yarin da su yi kokarin yin amfani da su wajen tsaftace wurin zamansu.

Mataimakin shugaban gidan yarin wanda kuma ya karbi kayan agajin Mr Muhammed ya nuna godiyarsa kuma ya dauki alkawarin cewa za su yi amfani da kayan da aka kawo musu ta hanyoyin da ya kamata. Kayan sun hada da kwalayen magungunan feshi da sabulan wanka da dai sauran su.

Share.

game da Author