Cibiyar kiwon lafiya dake Kuchigoro Abuja ta fara aiki mako biyu da gama gyaranta.
Asibitin na daya daga cikin asibitoci 10,000 wanda gwamnati zata gyara a cikin wannan shekarar.
Da ya ke jawabinsa a wajen taron bude cibiyar, Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce dalilin gyara wadannan cibiyoyin kiwon lafiya saboda mutane a duk inda suke a kasa Najeriya su iya samun ingantacciyar kiwon lafiya musamman talakawa.
Ya kuma nuna farin cikinsa lokacin da ya ziyarci asibitin inda ya ga cewa mutane da yawansu na samun kula a asibitin.
Bayan haka daya daga cikin ayukkan asibitin shine kula da masu juna biyu da kuma yara jirajirai.
Bangarorin da aka gyara a asibitin sun kunshi; Sashen bada tazaran iyali, Sashen yin rigakafin yara da kuma awon ciki, inda ake gwagin cutar tarin fuka, dakin haihuwa, dakin masu jego da kuma motar daukan mara lafiya wato Amblulance Kenan da turance.