Bani ne na ce ofishin jakadancin Najeriya tayi mini hidima ba – Inji Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta amince cewa lallai ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Ingila tayi mata hidima da kudade masu yawa a duk lokacin da ta kai ziyara kasar Ingila.

Daga farko dai Aisha Buhari ta musanta hakan sai gashi yanzu kuma ta ce hakan da akayi mata dai dai ne a matsayinta na uwargidan shugaban Kasa.

Bayanai ya nuna cewa ofishin jakadancin Najeriya ta kashe mata kudade da ya Kai fan 15,000 a wajen tarban ta tun daga filin jirgi saman kasar zuwa masauki.

Bayan haka kuma ofishin ta sake irin wannan hidima a wata zuwa da tayi tare da wadansu matan gwamnoni su 10 inda ta kashe ma kowani daya daga cikinsu fan 1500 domin tarba da masuki.

Share.

game da Author