Mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkar Majalisar dattawa Ita Enang ya ce bashi da wata masaniya akan cewa da keyi wai Buhari ya sake mika sunan Ibrahim Magu majalisar dattawa domin sake tantanceshi da amincewa da shi a matsayin shugaban hukumar EFCC ba.
Ita Enang ya ce sau uku ana kiransa daga wasu kafofin domin samun tabbacin hakan.
Ya ce ko da hakan zai taso toh shine kan gaba wajen ganin hakan ya yiwu amma har zuwa yanzu bashi da wata masaniya akan hakan.
An ce Buhari ya sanya hannu a takardar sake mika sunan Magu gabar majalisar sannan ya bari ma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari domin mika wa gaban majalisar kafin ya tafi hutu kasar Ingila.