Babban asibiti da ke yankin Wuse, Abuja ta sanar da rufe asibitin na kwanaki 4 domin gudanar da feshin kwari da ta saba yi a kowane shekara.
Hukumar asibitin tace ta na yin hakanne domin samarda kariya ga majinyata da kuma ma’aikatan asibitin.
Tace zata yi fara feshin ne daga 26 zuwa 29 na watan Janairu shekarar 2017.
Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta sami labarin cewa hukumar asibitin ta bada umurin cewa kada a sake karban maralafiya sannan wadanda suke kwance a asibitin an sallame su tun daga makon da ya gabata.
Duk da cewa ma’aikaciya wannan gidan jaridar ta PREMIUM TIMES ta yi kokarin samun cikaken dalin yin wannan feshi cikin gaggawa daga wurin shugaban asibitin y ace ba abin da zai faga akan maganar.
Bayan haka bincike ya nuna cewa sauran asibitocin da ke cikin garin Abuja na yin feshi kowane shekara kuma dakatar da aiki suke yi idan za su yi.