Reshen kungiyar malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha ta KadPoly ta ce ba za ta bi kiran da uwar kungiyar ta yi ba na duk kwalejojin su shiga yajin aiki daga yau litinin ba.
Reshen kungiyar na KadPoly ta ce ba za ta bi uwar kungiyar ba saboda ba ta shawarce ta ba akan fara yajin aikin.
Aliyu Ibrahim, shugban kungiyar malaman kwalejin KadPoly ya kara da cewa reshen kungiyar ba ta da wata masaniya akan shirin yajin aikin saboda haka ba za su bi kiran uwar kungiyar ba.
Shugaban kungiyar malaman na kasa, Usman Dutse, ya ce kungiyar ta ba da sanarwan rufe duka kwalejojin kimiyya da fasaha na kasa Najeriya ne a taron ta da tayi a makon da ya wuce.
Yace za’a fara yajin aikinne daga yau zuwa 6 ga watan Fabrairu domin tunasar da gwamnati akan alkawuran da ta dauka akan kwalejojin da har yanzu ba ta cika ba.
A Kaduna kuma, Kwalejin ta ce kowani dalibi ya zo makaranta domin cigaba da karatunsa.