Ba za mu sake duba wani dansanda ko iyalinsa ba a jihar Zamfara – Inji Kungiyar Likitocin

1

Shugaban Kungiyan likitocin Najeriya reshen jihar Zamfara, Tijjani Abubakar da sakataran kungiyar Mannir Bature sun umurci likitocin jihar da kada su sake duba wani ‘dan sandan jihar ko iyalansa saboda abinda sukayi ma wani likita a shekaran da ya gabata.

Kwamishanan ‘yan sandan jihar Zamfara Shaba Alkali ya roki kungiyar da ta sassauta akan wannan hukuncin musamman yadda lamarin ya shafi kiwon lafiyar mata da yara.

Kwamishinan yace ya kamata kafin likitocin su yanke wannan shawara su dan tattauna dasu akan matsalar kafin daukar wannan mataki.

Ya roke su da su yi hakuri su zo a zauna domin samun maslaha akan hakan.

Share.

game da Author